in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a girmama iko da moriyar jama'ar Ukraine, in ji kasar Sin
2014-03-06 20:59:21 cri
Kasar Sin tace ya kamata a girmama da kuma kula da iko da moriyar jama'ar kasar Ukraine ta kabilu daban daban bisa doka, sannan a yi la'akari da bukatun bangarori daban dabanmasu ruwa da tsaki yadda ya kamata.

kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Qin Gang yayi bayanin haka a yau Alhamis 6 ga wata lokacin ganawar sa manema labarai da aka saba yi duk rana .

A wani labarin kuma kamfanin dillancin labaru na Interfax na kasar Ukraine ya ba da labarin cewa, a yau majalisar dokokin kasar Crimea mai cin gashin kanta ta zartas da kudurin cewa, za ta shiga tarayyar Rasha bisa wani matsayi mai zaman kai, kuma za a jefa kuri'ar raba gardama kan matsayin kasar a ranar 16 ga wata a maimakon ranar 30 ga wata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China