A wannan rana, hare-hare mafi muni sun faru ne a lardin Anbar dake yammacin kasar, hare-haren guda hudu da aka kai a manyan biranen Ramadi da kuma Fallujah da rundunonin sojojin tsaro sun haddasa rasuwar sojoji guda 18, yayin da guda 22 suka ji rauni. Lardin Anbar da ke iyaka da kasar Syria, ya sha gamuwa da hare-haren kungiyar Al-Qaida da suke kaiwa kan rundunonin sojoji dake lardin. Kuma tun a watan Janairu na shekarar bana, ake ci gaba da fuskantar tabarbarewar yanayin tsaro a lardin na Anbar, musamman a yankin, Fallujah da ke hannun kungiyar Al-Qaida da kuma kungiyar da ke adawa da gwamnati.
Bugu da kari, dan takardar majalisar dokokin kasar ta Iraki Mohammed Hussein Hamid al-Gawamid ya rasu a sanadiyyar harin da wasu dakarun da ba a san asalinsu ba suka kaiwa motarsa. Mr. al-Gawamid shi ne dan takara na biyu da aka kai wa hari kafin a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar da za a yi a ran 30 ga watan Afrilun shekarar bana. (Maryam)