Wani mai samun sako daga 'yan sandan kasar Iraki ya bayyana cewa, a yankin Tuz Khourmatu dake da tazarar kilomita 170 daga Baghdad a arewa, an kai jerin hare-haren boma-bomai na kunar bakin wake a cikin mota da kuma gefen hanya a kusa da wani masallaci na darikar Shia a daren Asabar, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, yayin da wasu 72 suka jikkata. Yankin Tuz Khourmatu na kasancewa a arewa maso gabashin jihar Salaheddin, inda Larabawa, kurdawa, da kuma 'yan Turkmen suke zama tare. Lamarin dake janyo rikicin addini lokaci zuwa lokaci tsakanin al'ummomi mazauna wurin, haka kuma yankin na fama da hare haren ta'addanci a kai a kai.
Ban da haka, a wannan rana, an yi harbe-harbe sau da dama a birnin Baghdad, da Tal Afar dake arewa maso yammacin Baghdad, da birnin Baqouba, hedkwatar jihar Diyala dake gabashin kasar, da kuma birnin Mosul, hedkwatar jihar Nineveh dake arewacin kasar Iraki, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da kuma jikkata wasu da dama.(Fatima)