Hukumar 'yan sanda na kasar Iraki ya bayyana a ran lahadi 15 ga wata cewa, a wannan rana an samu hare-haren ta'addanci da dama a kasar, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 16 tare da jikkata wasu 36.
Wani majiya na 'yan sandan kasar ya ce, a ranar a jere ne aka kai farmaki ta hanyar tada bomai-bomai a cikin wassu motoci a kalla 4 a garin Sadr da yankin Husseiniya da ke birnin Bagadaza, babban birnin kasar, wadanda suka haddasa mutuwar mutane a kalla 8 tare da saura 35 suka jikata.
A birnin Sa'diyah da ke arewa maso gabashin birnin Bagadaza, wasu dakaru da ba a san asalinsu ba sun tada bom da aka dasa a cikin wani gida, sakamakon haka mutane 5 da ke zama a cikin gidan dukkansu sun mutu.
Haka kuma a birnin Mosul da ke arewa da Bagadaza, an harbe wata Ma'aikaciyar gidan talibijin har lahira. Ban da wannan kuma, an samu farmakin ta'addanci da dama a garin Baquba, babban birnin jihar Diyala da ke gabashin kasar Iraki, wadanda suka sanya mutane 2 suka rasa rayukansu sanna mutum daya ya jikata.(Danladi)