Mahukuntar 'yan sanda na kasar Iraki sun bayyana a ran Alhamis 14 ga wata cewa, an kai hare-hare da dama ga musulmai mabiya darikar Shi'ite a wannan rana, abin da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 36, tare da jikkata mutane 86.
A shekarar bana dai, an samu hare haren ta'addanci a Iraki da dama, wadanda suka jefa kasar cikin wani mummunan hali. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, daga watan Janairu zuwa Oktoba na bana, yawan farar hula da suka mutu ya kai kusan dubu 7 tare da sauran wadansu dubu 16 da suka ji rauni.(Danladi)