Mutane 78 suka mutu a yayin da 166 suka jikkata a wasu sabbin tashe tashen hankali a kasar Iraki
A kalla mutane 78 aka kashe a yayin da 166 suka jikkata a cikin jerin hare hare a kasar Iraki a ranar Asabar, wanda ya hada da wani harin kunar bakin wake na bam da ya shafi wasu masu ibada 'yan shi'a a Bagadaza, hedkwatar kasar Iraki, a cewar 'yan sanda da kafofin watsa labarai na wurin. A kalla mutane 51 suka mutu sannan 107 suka ji rauni a ranar Asabar da yamma a yayin da wani dan kunar bakin wake ya ta da bam din dake jikinsa a tsakiyar tarin jama'a 'yan shi'a a unguwar Adamiya dake arewacin Bagadaza, a cewar wani dan sanda da ya bukaci a sakaya sunansa a yayin da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Wadannan mutane na kan hanyar zuwa wani masallacin unguwar Kadhimiya dake arewacin Bagadaza, in ji wannan dan sanda.
Haka kuma a ranar ta Asabar da yamma, mutane a kalla 11 suka mutu yayin da 35 suka ji rauni a lokacin da wata mota da aka dana bam ta tarwatse a kusa da wani dakin shan kofi na birnin Balad mai tazarar kilomita 80 a arewacin Bagadaza, a cewar wata majiyar 'yan sanda tare da bayyana cewa wani dan sanda guda ya mutu kana biyu suka jikkata a yayin da wata nakiya tashi a kan hanya a lokacin wucewa motar jami'an tsaro dake sintiri a birnin Mashahda mai tazarar kilomita 30 da birnin Bagdad. (Maman Ada)