Wang Yi ya fara ziyarar aiki ne a kasar ta Iraki a wannan rana da safe. Wannan shi ne karo na farko da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai ziyara a kasar Iraki cikin shekaru 23 da suka wuce. A lokacin ziyararsa, mista Wang zai yi shawarwari da takwaransa na kasar Hoshyar Zebari tare da ganawa da shugaban majalisar dokokin kasar Osama al-Nujaifi.(Tasallah)