Bangaren 'yan sanda na kasar Iraki ya bayyana a ran 7 ga wata cewa, an samu fashewar bam na kunar bakin wake a wani sansanin soja da ke tsakiyar Iraki, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 15, tare da raunata sauran mutane 45.
Wani majiya na bangaren 'yan sanda na Iraki ya gaya wa kafofin watsa labaru cewa, da karfe 10 da rabi na daren ran nan, a garin Tarmiyah da ke da kilomita 30 da ke arewa da birnin Bagadaza, babban birnin Iraki, mutane biyu sun tuka motoci guda biyu da aka tada boma-bomai a ciki, bi da bi ne suka kutsa cikin wani sansanin da suka tada boma-bomai. Yawancin mutanen da suka mutu ko ji rauni sojojin Iraki ne.
Ya zuwa yanzu babu wani ko wata kungiyar da ta dauki nauyin aikata wannan al'amari.
A ranan da safe, an kai hare-haren nuna karfin tuwo a wurare da dama ciki har da Bagadaza a Iraki, sakamakon haka mutane a kalla 12 sun mutu, tare da sauran mutane 23 suka ji rauni.(Danladi)