Sanarwar ta bayyana cewa, wasu dakaru ne suka shiga gidajen ma'aikatan hukumar a birnin Ndele dake arewacin kasar Afirka ta Tsakiya, a lokacin, akwai ma'aikata hudu a cikin gidajen, inda dakarun suka kashe daya dake cikinsu, kana guda ukun suka tsira da rayukansu.
Wakilin hukumar dake jamhuriyar kasar Afrirka ta Tsakiya ya yi allah wadai da lamarin. Ya kuma yi kira da bangarorin da abin ya shafa a kasar Afirka ta Tsakiya da su kiyaye dokokin kasa da kasa yadda ya kamata, don ba da tabbaci ga ayyukan ma'aikatan jin kai.
A kwanan baya, yanayin tsaro ya tabarbare a kasar Afrika ta Tsakiya sakamakon fadace-fadacen ke kawo cikas ga ayyukan taimakon jin kai ga jama'ar kasar. (Maryam)