Bisa labarin da kafofin watsa labarun kasar Afirka ta Tsakiya suka watsa, yanzu haka karin sojoji 400 da gwamnatin Faransa ta tura zuwa kasar sun riga sun isa birnin Bangui, babban birnin kasar da safiyar ranar Alhamis 27 ga wata. Matakin da ya sanya adadadin sojojin Faransa a kasar kaiwa dubu biyu.
An ce wadannan sojoji da suka shiga kasar Afirka ta Tsakiyan daga makwabciya kasar Chadi, cikin jerin gwanon motoci masu sulki 50, da sauran manyan motocin soji, za su gudanar da aikin ba da taimako ne ga matakin soja da ake dauka a kasar.
Rahotanni da dama sun ce shugaban kasar Faransa Francois Hollande, shi ma zai isa birnin Bangui a ran 28 ga wata. Yayin ziyarar da zai gudanar, shugaba Hollande zai gabatar da wani jawabi ga sojojin kasarsa da ke Afirka ta Tsakiyan, haka kuma zai yi shawarwari da shugabar wucin gadin kasar Madam Catherine Samba Panza. (Danladi)