in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi maraba da kasar Afirka ta tsakiya ta kafa sabuwar gwamnati
2014-01-29 14:59:15 cri

A ran 28 ga wata, babban Magatakardar MDD Mista Ban Ki-Moon ya bayar da wata sanarwa ta kakakinsa, inda ya yi maraba da gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya ta kafa wata sabuwar gwamnati, sannan ya taya shugaban wucin gadi na kasar Madam Catherine Samba-Panza, da firaministan gwamnatin wucin gadi Mista Andre Nzapayeke murna a kan haka.

Mr Ban Ki-Moon ya ce ya yi imanin cewa, kafuwar sabuwar gwamnati za ta samar da wata kyakkyawar dama ga yunkurin siyasa na kasar, har ila yau ya sake nanata kudurin MDD na son nuna goyon baya ga hukumar wucin gadi ta kasar Afirka ta Tsakiya wajen tabbatar da zaman lafiyar jama'a da moriyarsu.

Sai dai a wani bangaren kuma, babban Magatakardar Majalissar ya nuna damuwa game da ricikin nuna karfin tuwo da ya dade ana nunawa a kasar, wanda ya haifar yanayin jin kai da shafi rabin jama'a a kasar, don haka sai ya yi kira ga bangarorin da rikicin ya shafa na gida da waje, da su ci gaba da yin kokari domin kawo karshen tashin hankalin.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China