Kakakin asusun kula da yara na MDD Marixie Mercado ya bayyana cewa, a halin yanzu, dakarun "Seleka" da kuma na gwamnatin kasar dukkansu suna amfani da kananan yara a matsayin sojoji. Kwanan baya, gwamnatin wucin gadi ta jamhuriyar kasar Afirka ta Tsakiya ta amince wakilan MDD su shiga sansanonin kungiyoyin dakarun kasar, lamarin ya sa, aka saki wasu daga cikin yaran.
Bisa labarin da muka samu, an ce irin wadannan kanana yara da aka saki a wannan karo sun hada da yara mata guda 6, da yara maza guda 17, wadanda shekarunsu ya kama daga 14 zuwa 17. Kuma asusun na Unicef ya bayyana cewa, ana kula da wadannan yara a wuri mai tsaro.
Kuma bisa wani sabon hasashen da asusun ya yi, mai iyuwa ne, yawan kananan yaran da aka sanya aikin soja a kasar Afirka ta Tsakiya ya kai dubu 6, don haka, asusun ya yi kira ga kungiyoyin dake dauke da makamai na kasar Afirka ta Tsakiya da su saki dukkan kanana yaran da suka dauka a matsayin sojoji. (Maryam)