Fadar shugaban kasar Faransan ta fidda wata sanarwa, dake cewa shugaba Francois Hollande ya gabatar da wani taro kan tsaron kasa, wanda ya maida hankali kan bukatar babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ta kara yawan sojoji zuwa kasar Afirka ta Tsakiya, a yunkurin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a kasar.
Sanarwar ta ce, sojojin da za a tura sun hada da sojojin yaki, da 'yan sandan soji. Ana kuma sa ran sojojin za su yi hadin gwiwa da takwarorin su na kasashe mambobin kungiyar tarayyar turai ta EU, a aikin da zasu gudanar.
Baya ga wannan, sanarwar ta kara da cewa, Faransa ta yi kira ga kasashen duniya da su kara goyon bayan da suke baiwa Afirka ta Tsakiya, tare da kira ga kwamitin sulhun MDD, da ya hanzarta aikin jibge sojan kiyaye zaman lafiya a kasar. Haka zalika Faransa ta yi kira ga kungiyar EU, da ta kara yawan nata sojojin, ciki har da 'yan sandan sojin kungiyar.
Faransa ta yi marhabin, da goyon bayan da kasashen nahiyar Afirka ke baiwa kungiyar ba da taimako ta kasa da kasa, karkashin jagorancin kungiyar tarayyar kasashen Afirka, da fatan wannan kungiya za ta kara fadada kwazon ta game da wannan muhimmin aiki. (Fatima)