in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 11 sun mutu sakamakon hargitsi a Bangui na Afirka ta Tsakiya a kwanaki 2
2014-02-27 21:00:07 cri
Ranar 26 ga wata bisa agogon wurin, wani jami'in kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta kasar Afirka ta Tsakiya ya ce, daga safiyar ranar 25 ga wata zuwa daren ranar 26 ga wata, kungiyar ta tattara gawawwaki guda 11 a birnin Bangui, hedkwatar kasar, ciki had da wasu da aka daddatsa.

Jami'in ya kara da cewa, tun daga ranar 5 ga watan Disamban da ya gabata, kungiyar ta tattara gawawwaki guda 1240 a birnin na Bangui. Yana ganin cewa, hakikakin yawan wadanda suka mutu sakamakon hargitsin zai wuce yadda kungiyar ta kidaya, saboda iyalan wasu mamata sun tafi da gawawwakin 'yan uwansu, kana kuma wasu gawawwaki sun bace sakamakon wasu dalilai. Har wa yau kungiyar ba ta kidaya yawan mutanen da suka mutu sakamakon hargitsin da ya barke a sauran lardunan kasar ba. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China