A yayin taron da kwamitin sulhu ya kira a wannan rana dangane da halin da ake ciki a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Mr. Ban ya bayyana cewa, cikin shekarar da ta wuce, ayyukan hukumomin kasar sun tsaya ciki sakamakon juyin mulkin da aka yi a Afirka ta Tsakiya, mabiya addinai daban daban sun shiga tashin hankali, lamarin da ya kusan kawo raba wannan kasa. A halin yanzu, kimanin 'yan gudun hijira miliyan 1 ne ba su da wuraren zama, mutane sama da miliyan 2.5 na bukatar taimakon jin kai. Mr. Ban ya ce, zai ba da shawara ga kwamitin sulhu wajen tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Afirka ta Tsakiya cikin sauri, kana ana bukatar watanni da dama wajen gudanar da wannan aiki.
Rahotanni na cewa, a halin yanzu, akwai sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU guda dubu shida a kasar Afirka ta Tsakiya, yayin da kasar Faransa ke da dubu daya da dari shida a kasar. Bugu da kari, a ran 14 ga wata, kasar Faransa ta sanar da kara tura sojoji dari 4 zuwa kasar, yayin da kungiyar EU za ta aike da sojoji dubu 1 zuwa kasar. (Maryam)