Mr. Keita ya yi wannan furuci ne lokacin da yake ganawa da shugaban kamfanin Hanergy na kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Mali. Kuma ya bayyana cewa, kasar Mali na maraba da kamfanin Hanergy da ya zuba jari wajen gina tasha ko kamfanin samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana, ta yadda za a iya bunkasa tattalin arzikin kasar Mali, samar da karin makamashi ga wurin da kuma karin guraban aikin yi domin kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar. (Sanusi Chen)