in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a Mali
2014-01-17 20:29:49 cri
Kasar Sin ta tura dakarun wanzar da zaman lafiya 395 da za su yi aiki da tawagar wanzar da zama lafiya ta MDD da ke Mali.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ne ya bayyana hakan yayin taron manema a nan birnin Bejing, inda ya ce, dakarun da kasar Sin ta aika, sun kunshi jami'an tsaro 170, sojoji injiniyoyi 155 da ma'aikatan lafiya 70.

Hong Lei ya ce, kasancewar kasar Sin mamban din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, tana goyon bayan muhimmiyar rawar da MDD ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya. Yana mai cewa, ayyukan tabbatar da zama lafiya, wasu muhimman hanyoyi ne na sassanta batutuwan shiyya-shiyya.

Don haka, kasar Sin tana goyon baya tare da shiga a dama da ita cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.

Ya ce, kasar Sin ta shiga aikin wanzar da zaman lafiya na MDD a Mali ne ba kawai don ta taimakawa MDD ba, har ma ta bayar da gudummawa wajen bunkasa zaman lafiya da tsaro a Afirka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China