in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a warware rikicin Ukraine ta hanyar shawarwari, in ji wakilin Sin
2014-03-04 15:12:57 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi, ya yi kira ga bangarorin daban daban da rikicin kasar Ukraine ya shafa da su kokarta kawo karshen rikicin ta hanyar yin shawarwari, don kiyaye zaman lafiya da zaman karko a yankin.

Mr. Liu ya bayyana hakan ne a jiya Litinin 3 ga wata, yayin zaman kwamitin sulhu na MDD, wanda aka kira musamman don tattauna wannan batu na kasar Ukraine. Har wa yau Liu ya ce kasar Sin na ci gaba da yin kira ga kasar Ukraine da ta warware rikicin dake wakana bisa tsarin dokokin kasar kuma cikin lumana.

Mr. Liu ya bayyana cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kiyaye ka'idojin hana kutsa kai cikin harkokin gidan kasashen ketare, da girmama 'yanci da mulkin kai na kasar Ukraine. Kana, za ta ci gaba da mai da hankali kan yanayin kasar Ukraine a nan gaba, tare da yin kira ga bangarorin daban daban da lamarin ya shafa da su girmama dokokin kasa da kasa, su kuma warware bambancin ra'ayinsu ta hanyar siyasa da kiyaye zaman karko a yankin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China