Da yake amsa tambayoyi game da matsayin kasar Rasha a cikin wannan lamari, yace kasar Sin tana tsaye akan ka'idojin ta na diflomasiyya da tsarin huldar ta da kasashen waje kuma akan haka ne take tafiyar da al'amurran dake wakana a kasar Ukraine.
Mr Qin ya ce bayan haka kuma Sin tana bin yadda al'amurra suke a tarihi da dalilai na yanayin da ake ciki baki daya game da batun na kasar Ukraine wajen tsayawa a matsayin ta.
Wadannan bayanai dai sun zo ne a matsayin Karin haske game da bukatar kasar Sin da shi kakakin ma'aikatar harkokin wajen ya gabatar inda yace ya kamata duk bangarorin da lamarin Ukraine ya shafa su bi dokokin kasa da kasa wajen warware matsalar da suke fuskanta a siyasance ta hanyar tattaunawa da sulhu. (Fatimah Jibril)