Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da ya kai ziyarar aiki a birnin Bagadaza na kasar Iraki ranar Lahadin nan 23 ga wata ya ce, kasarsa a shirye take ta inganta duk wata hanyar hadin gwiwa da Iraki, ta zurfafa mutunta juna a siyasance, sannan ta yi amfani da damar da kowanensu ke da ita wajen karfafa hadin gwiwar tattalin arzikin juna.
Mr. Wang ya furta hakan ne a lokacin da ya gana da firaministan kasar ta Iraki Nuri al-Maliki.
Shi ma a nashi martanin Nuri al-Maliki ya godewa kasar Sin bisa ga goyon bayan da ta dade tana ba kasarsa wajen sake gina ta.
Haka kuma a ganawar da ya yi da takwaransa Hoshyar Zebari, Mr. Wang ya ce, kasar Iraki abokiyar arziki ce, kuma abin dogara da ita a yankin Gabas ta Tsakiya, ya kara da cewa, kasarsa a shirye take ta inganta cudanya tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, kuma za ta cigaba da goyon bayan shirin mika mulki da take yi, tare da ba da gudunmuwa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.
Da yake mai da martini, Hoshyar Zebari ya jaddada cewa, kasarsa tana nan a kan amincewa da tsarin kasar Sin a matsayin kasar daya tak, kuma tana goyon bayan Sin a kan batutuwa da suka shafi babbar moriyar kasar.
A lokacin ziyarar tashi ta yini daya, Mr. Wang ya gana da kakakin majalissar wakilan kasar Osama al-Nujaifi.
Ministan harkokin wajen na kasar Sin ya isa birnin Bagadaza ne a safiyar jiya Lahadi bisa goron gayyatar da takwaransa Hoshyar Zebari ya mika masa, abin da ya sa ziyarar ta zama ta farko da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai kasar a cikin shekaru 23 da suka gabata. (Fatimah)