Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wang Min, ya ce, wajibi ne a sanya batun yaki da talauci a sahun gaba, cikin jerin kudirorin cimma muradun karni ko MGDs bayan shekarar 2015.
Mr. Wang ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin taron majalissar tattauna batutuwan tattalin arziki da zamantakewa, da suka shafi shirye-shiryen samar da ci gaba na shekarar 2014.
Wakilin na kasar Sin ya ce, yaki da fatara, na cikin manyan kalubale da duniya ke fuskanta, kuma aiki ne da ya wajaba a sanya gaba, muddin dai ana burin samar da ci gaba mai dorewa.
Da yake tsokaci kan kudurin shirin cimma muradun karni na tabbatar da ci gaban daukacin sassan duniya, Mr. Wang ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na baiwa shirin na MDGs cikakken goyon baya, ta hanyar ba da tata gudummawa ga shirye-shiryen wanzar da ci gaba.
Ana dai fatan sabon shirin na MDGs wanda za a aiwatar bayan shekarar 2015, zai maye gurbin kudurorin nan 8, da ake burin kammalar su nan da shekarar ta 2015. (Saminu)