140112bagwai
|
An dai tsara gudanar da taron ne a ranar 15 ga wannan wata karkashin jagorancin shugaban tarayyar Najeriya Mr. Goodluck Jonathan a Legas.
Shugaban Majalissar Malamai na kungiyar ta Izala Sheik Muhammadu Sani Yahaya Jingir shi ne ya tabbatar da kauracewar taro lokacin daya zantawa da gidan rediyon CRI ta wayar tarho a Kano jim kadan kafin tashin sa zuwa kasar Saudiya domin aikin Umra.
Sheik Sani Yahaya yace ko kadan bada yawun su aka gudanar da shi wannan taron mai taken Zaman Lafiya da Hadin kai ba domin samun cigaba mai dorewa.
Ya zargi wadanda suka shirya taron da laifin zubar da mutuncin kungiya ga `yan Siyasa, lamarin da ya ce cin fuska ne ga addinin Islama.
Yace makasudin assasa kungiyar shi ne ilimintar da al`ummar musulmi tanade tanaden addinin musulunci, amma ba shiga harkokin siyasa ba.
Malamin ya cigaba dacewa, manufar taron da ake kokarin gudanarwa ita ce yada manufar wasu mutane na daban dake cikin gwamnati, a dai dai lokaci da ake fuskantar matsalolin rashin tsaro a kasa.
Sheik Muhammadu Sani Yahaya Jingir yace har yanzu kungiyar tana dunkule wasu kalilan ne kawai suke neman kaucewa alkiblar da kungiyar ta sanya a gaba na ilimintarwa don tabbatar da ganin al`ummar Musulmi suna aiki da sunnar Manzon Allah Annabi Muhammadu S.A.W.
To ko mene ne madogarar Malamin na zargin daya keyi nacewa `Yan siyasa na amfani da wasu `ya `yan kungiyar musamman akan shi wannan taro da kungiyar zata gudanar? Sheik Sani Yahaya Jingir yace gayyatar Jonathan na daya daga hujjar kasancewa babu abin daya hada shugaban da addinin Musulunci amma kuma aka sanya shi a matsayin shugaban taro.
Ya zargi Jagoran taron Sheik Bala Lau da amfani da mukaminsa da kuma sunan kungiya wajen cimma wasu burikan sa na daban.
Daga karshe ya yi kira ga `yan jaridu dasu kara jajircewa sosai wajen tabbatar da haduwar kan al`ummar musulmin Najeriya, ta hanyar ba da rahotannin da baza su haifar da rarrabuwar kawuna ba.(Garba Abdullahi Bagwai)