Gobara ta lashe dukiyoyin da aka kiyasta sun haura naira miliyan 100, a shahararriyar kasuwar nan ta Kara, dake cikin garin Sokoto, arewacin Najeriya. Wakilinmu dake Najeriya Murtala na dauke da karin bayani.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya rawaito cewa, gobarar ta tashi ne a tsakiyar daren jiya Talata, wadda aka alakanta tashinta da haduwar wayoyin wutar lantarki. Gobarar ta ci gaba da ci har zuwa karfe shida da rabi na safiyar yau.
Wasu daga cikin 'yan kasuwar sun samu damar kubutar da kayayyakinsu, yayin da wasu ba su samu damar hakan ba, haka kuma wasu masu shaguna a kasuwar sun fito don yin gadin shagunansu daga farmakin bata-gari da barayi.
Alhaji Harande Chedi, Daraktan hukumar kashe gobara a jihar ta Sokoto, ya tabbatar da faruwar al'amarin, inda ya bayyana cewa ba a samu asarar rayuka ko raunuka a yayin gobarar ba.
Wasu daga cikin kayayyakin da ake sayarwa a kasuwar ta Kara sun hada da gero, dawa, masara, alkama, albasa, goro, da sauran kayan noma da kuma kayan amfani na yau da kullum.
Na samu damar zantawa da wani dan kasuwa mai sayar da maganin kwari a kasuwar Kara ta wayar tarho, don jin ta bakinsa game da wannan bala'i.
140205murtala gobara.m4a
|