Bisa labarin da aka bayar, an ce, a wannan rana, Faransa ta jibge motocin sulke da dama a birnin Bangui, hedkwatar kasar Afirka ta Tsakiya domin tabbatar da tsaro.
A ranar alhamis 9 ga wata, kungiyar ECCAS ta kira taron shugabanni na tsawon yini biyu a birnin N'Djamena, na kasar Chadi, domin yin shawarwari kan yadda za a tinkari yanayin da ake ciki a yanzu da yanayi a nan gaba. A jawabin sa bayan taron babban sakataren kungiyar ECCAS, Ahmat Allami ya ce, idan gwamnatin rikon kwarya da shugabannin kasar ba za su iya daidaita rikici da ake yi cikin watanni da suka gabata ba, kamata ya yi su yi murabus. Kuma sakamakon haka a jiya, kungiyar ta sanar da cewa, shugaba Djotodia da firaminista Tiengaye sun yi murabus.
A sakamakon tangal-tangal na yanayin da ake ciki a birnin Bangui, yanzu rundunar sojan Faransa ta riga ta jibge motocin sulke a kalla hudu a birnin, tare da harbe harsashin gargadi, domin kauracewa abkuwar rikici tsakanin membobin kungiyar Seleka da na sauran kungiyoyi.(Fatima)