in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na son taimakawa Afirka ta Tsakiya wajen samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunkasuwa
2014-01-13 20:21:20 cri
Kasar Sin na fatan rukunonin siyasa na kasar Afirka ta Tsakiya za su kiyaye kwanciyar hankali da hadin kan al'ummar kasarsu, a kokarin kare babbar moriyar kasarsu da ta jama'arsu, kamar yadda madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a ranar 13 ga wata.

An labarta cewa, a kwanan baya, shugaban Afirka ta Tsakiya na wucin gadi da firaministan gwamnatin kasar sun yi murabus. Babacar Gaye, manzon musamman na MDD mai kula da harkokin Afirka ta Tsakiya ya yi kira ga al'ummar Afirka ta Tsakiya da su kai zuciya nesa, su goyi bayan kasashen duniy, a kokarin da suke yi na taimaka musu wajen kiyaye kwanciyar hankali a kasar.

A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, madam Hua ta ce, kasar Sin na son ci gaba da hada kai da kungiyar kawancen raya tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka da sauran kasashen duniya wajen taimakawa kasar Afirka ta Tsakiya wajen samun zaman lafiya, tsaro da bunkasuwa, gwargwadon karfinta.(Tasallah

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China