Ma'aikatar kula da harkokin tsaron kasar ta Nijeriya ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai, gwamnatin kasar ta cika alkawarinta na aikewa da sojojin kasa guda 1200 zuwa kasar Mali, bayan wadannan sojojin na karshe guda 162 sun isa kasar.
A ran 27 ga watan da ya gabata, yayin taron manema labarai da aka kira a birnin Abuja, kakakin kwamitin kula da labaran tsaron kasar Nijeriya ya nuna cewa, cikin wata guda da ya gabata, sakamakon fuskantar yanayin tabarbarewar tsaro a kasar, da kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi, musamman ma kungiyar Boko Haram suka haddasa, rundunar sojan kasar Nijeriya ta horas da sojojin musamman fiye da dubu 2, wajen yaki da su, amma a halin yanzu, Nijeriya ta riga ta aika da galibin sojojin zuwa wurare mafi fama da rikici a kasar Mali.
Bugu da kari, bayan kasar Faransa ta janye sojojinta guda dubu 4 daga kasar Mali a watan Maris, sojojin Nijeriya da ma sauran sojoji da kasashen Afirka suka tura wa kasar Mali za su kara taimaka cikin yakin, da kuma kiyaye zaman lafiya a kasar. (Maryam)