in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Gambia ta ki amincewa da zargin da ECOWAS ke mata kan zaben shugaban kasar
2011-11-25 11:28:58 cri
A ranar Alhamis din da ta gabata hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Gambia ta ki karbar zargin kungiyar tattalin arzikin Afrika ta yamma ECOWAS ke yi mata kan zaben shugaban kasar.

A sanarwar da kungiyar ta ECOWAS ta bayar a ranar Larabar da ta gabata, ta ce ba za ta aike da masu sa ido kan zaben shugaban kasar da za a yi ranar 24 ga watan Nuwamba saboda karancin doka da zai sa a yi zabe mai inganci.

Alhaji Mustapha Carayol shi ne shugaban hukumar zaben mai zaman kanta ta kasar Gambia ya bayyana sanarwa ta kungiyar ECOWAS a matsayin kage ne kawai.

Shugaban ya ce tsawon lokaci kasar Gambia na da duk muhimman abubuwan da ake bukata a fagen siyasa kama daga yin rigistar masu zabe, katin zabe, bude lokacin takara har tsahon lokacin da za a yi zabe. Amma duk da haka kungiyar ta ECOWAS ta ce ba za ta aiko da masu sa ido gun zaben ba, kuma bayan ta zargi gwamnatin Gambia da ma'aikatan gwamnati da hafsoshin soji suke neman shiga babban zaben da za a yi a kasar. (SALAMATU)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China