in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan kasar Rasha sun yi sharhi game da ziyarar shugaban kasar Sin a Sochi
2014-02-08 11:12:29 cri
A ranar Jumma'a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Sochi da ke yankin kudancin kasar Rasha, kuma ya halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi na Sochi na shekarar 2014, lamarin da ya jawo hankalin jama'a sosai. Kafofin yada labaru na Rasha suna sa ran game da shirin yin shawarwari har sau 5 da ke tsakanin shugabannin kasashen biyu a shekarar 2014 da shugaban Putin ya gabatar, kuma 'yan kasuwan Rasha sun fi mai da hankali sosai game da hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen Sin da Rasha.

Tun lokacin da shugaba Xi ya fara ziyarar, kafofin yada labaru na Rasha suke ta bayar da rahotanni game da ziyarar tasa a Rasha. A ranar 6 ga wata, a daren da shugabannin kasashen biyu suka yi shawarwari, kafofin yada labaru na Rasha sun sanar da wasu abubuwan da ke kunshe cikin shawarwarin nasu cikin sauri.

Bayan shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka yi, shugaban kamfanin man fetur na Rasha Igori Sechin ya bayyana cewa, a yayin taron, shugabannin biyu sun tattauna batun inganta hadin gwiwa a fannin makamashi a tsakaninsu. Sechin ya ce, Putin ya yaba wa dangantakar tattalin arziki da ke tsakanin kasashen Rasha da Sin, kuma ya ce, an samu babban ci gaba a wannan fanni. Daga bisani kuma, kamfanin man fetur na Rasha ya ba da wata sanarwa game da bayanan da shawarwarin ya kunsa.

A ranar 7 ga wata, jaridar Gazeta ta Rasha ta ruwaito ofishin yada labaru na fadar shugaban kasar na bayani game da shawarwarin shugabannin kasashen biyu, inda ta yi sharhi cewa, a yayin shawarwarin, Putin ya gabatar da wani shiri, wato za a kara tuntubawar juna a fannin siyasa, an kimanta cewa, za a yi shawarwari tsakanin shugabannin kasashen biyu har sau 5 a shekarar 2014, kuma ana sa ran sakamako mai kyau game da shirin. Ana kyautata zaton cewa, shugabannin kasashen biyu suna sa ran kasashen biyu za su cimma nasara a yayin gasar wasannin Olympics ta Sochi.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China