in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da magatakardan MDD
2014-02-07 16:30:48 cri
Ranar 7 ga wata, shugaba Xi Jinping ya gana da Ban Ki-moon, magatakarda na MDD a birnin Sochi na kasar Rasha.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya yaba wa muhimmiyar gudummawar da MDD take bayarwa wajen sa kaimi kan samun zaman lafiya da bunkasuwa a duniya. Ya kuma nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da mara wa MDD da magatakardan majalisar baya. Har wa yau shugaba Xi ya lura da cewa, kasar Sin ba za ta iya samun bunkasuwa ba, sai dai an samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a duniya. Don haka kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan kiyaye zaman lafiya, kara azama kan samun bunkasuwar tare, da raya hulda a tsakanin kasa da kasa. Ya ce, bunkasuwar kasar ta Sin za ta inganta karfin kiyaye zaman lafiya a kasa da kasa. Sa'an nan kuma, a matsayinta na wadda ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin za ta sauke nauyin da kasashen duniya suka sanya mata, za ta kara himma a ayyukan majalisar, za ta sa kaimi kan warware rikicin kasa da kasa cikin ruwan sanyi, a kokarin kara yin amfani da basirar Sinawa da karfin kasar Sin wajen kare zaman lafiya da tsaro a duniya, da kuma kara azama kan samun ci-gaban dan Adam.

A nasa bangaren shi ma, mista Ban ya ce, MDD ta yaba wa jagorantar da kasar Sin take yi a fannin daidaita kalubalolin da kasashen duniya suke fuskanta.

Haka zalika shugaba Xi ya yi bayani ga mista Ban game da halin da ake ciki a yankin arewa maso gabashin Asiya.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China