in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci a yi saurin komawa teburin shawarwari a Syria
2014-02-07 20:36:50 cri
Kasar Sin a tabakin kakakin ma'aikatar harkokin waje Hong Lei ta yi kira ga gwamnatin kasar Syriya da masu adawa da ita da su sake wani zaman tattaunawa ba tare da bata lokaci ba.

Hong Lei a ganawar da ya yi da manema labarai da aka saba yi duk rana a yau Jumma'a 7 ga wata a nan birnin Beijing, fadar gwamnatin kasar Sin, ya ce tabbatar da ci gaba da tattaunawa da samar da mafita a siyasance yana da matukar muhimmanci a yanzu.

Ya lura cewa da farko tattaunawar yana da wuya amma kuma aiwatarwa da aka yi a karon farko wani ci gaba ne mai kyau da ya fara nuna alamun nasara, don haka ya bukaci bangarorin biyu su yi kokari su zauna tare su tattauna sannan kowannensu ya aiwatar da nashi kokarin na ganin an samu mafita.

An dai kammala zagayen farko na tattaunawar a makon da ya gabata ba tare da wani ci gaba na a zo a gani ba kamar yadda mai shiga tsakanin na MDD da AL, Lahdar Brahimi ya nuna, yana mai bayyana cewa ya lura da matsaya daya da kowane bangare ya dauka.

A game da hakan kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hong Lei ya bukaci dukkan bangarorin biyu da su saurari shawarwarin Mr Brahimi da muhimmanci, shi kuma Mr. Brahimi a nasa bangaren ya bukaci a sake komawa teburin shawarwari a Geneva a ranar 10 ga wata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China