Madam Hua ta bayyana hakan ne yau Talata a nan birnin Beijing yayin taron manema labarai, inda ta ce, kasar Sin da sauran kasahen duniya, sun yi matukar kokari na ganin sassan biyu sun zauna tare a karon farko.
Ta bukaci sassan biyu da su kasance masu nuna hakuri da gaskiya, tana mai cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, tattaunawar za ta ci gaba muddin sassan biyu suka mutunta kudurin warware rikicin kasar a siyasance.
Don haka ta yi kira ga sassan biyu, da su nuna sadaukarwa bisa sanarwar Geneva, ta yadda za a daidaita bambance-bambancen da ke tsakaninsu, mutunta juna da gano hanyar matsalar kasar da dukkan bangarorin kasar za su amince da ita.
A ranar Litinin ne, manzon MDD da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa game da batun Syria, Lakhdar Brahimi ya bayyana cewa, wakilan sassan biyu, za su ci gaba da tattauna a yau Talata. (Ibrahim)