140201murtala.m4a
|
Kwanan baya, hukumar kiyaye hadarurruka tarayyar Najeriya reshen jihar Kano wato FRSC ta fitar da rahotonta game da hadarurrukan da suka faru a fadin jihar a cikin shekarar da ta gabata wato 2013, inda ta bayyana cewa mutane 2,499 ne hatsuran ya rutsa da su a bara.
Kwamandan hukumar a jihar kano, Alhaji Ibrahim Garba, ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran najeriya NAN cewar cikin wadanda hadarurrukan ya rutsa da su, 1692 maza ne, yayin da sauran 807 mata ne, sai dai ya ce hakan ba yana nufin maza sun fi mata yawan tuki ba.
Sa'annan ya kara da cewa, mutane 308 daga cikin wadanda hadarurrukan suka rutsa da su, sun rasa rayukansu, haka kuma 1484 ne suka samu raunuka.
Kwamanda Alhaji Ibrahim Garba ya ce motocin haya sun fi afkawa cikin hadarurrukan saboda fasinjoji ba sa jan hankalin direbobin da suke sheka gudun da ya wuce kima yayin da suka tuki. Sa'annan ya ce hukumar FRSC za ta ci gaba da fadakar da direbobin kan amfanin bin dokokin hanya, domin gujewa asarar rayukan al'umma.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.