in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mutane 24 yayin wasu hare hare a jihar Plateaun Nijeriya
2014-02-05 16:25:17 cri
Rahotanni daga Najeriya, sun ce a kalla mutane 24 ne wasu 'yan bindiga suka hallaka a kauyukan Atakar da Dajat dake yankin Ganawuri, a karamar hukumar Riyom dake Jihar Plateau.

Dan majalissar dokokin jihar ta Plateau mai wakiltar al'ummar Riyom Daniel Dem, ya tabbatarwa manema labaru aukuwar hare haren, wadanda wasu mahara da kawo yanzu ba a tantance ko su waye ba suka kaddamar a daren ranar Litinin. Ya ce ba ya ga wadanda suka rasa rayukansu, ragowar al'ummun kauyukan Biyu sun tsere zuwa makwaftan kauyuka dake kusa.

Har ila yau daga jihar Yobe dake Arewa maso Gabashin kasar ma, an tabbatar da rasuwar wasu mutane 19, sakamakon wani hari da wasu 'yan bindiga suka kaddamar a jihar.

A cewar kwamishinan 'yan sandan jihar ta Yobe Sanusi Rufa'i, kawo yanzu ba a tabbatar da ko 'yan kungiyar nan ta Boko Haram ne suka kai harin ba. Wannan hari na baya bayan nan ya zo gaf da alwashin da sabon shugaban rundunar sojin kasar Alex Badeh ya yi, na kawo karshen ayyukan kungiyar Jama'atu Ahlus-Sunnah Lidda'awati Wal-Jiha, wadda aka fi sani da Boko Haram.

Jihar Yobe dai na cikin jahohin kasar 3 dake karkashin dokar ta baci, wadda fadar gwamnatin kasar ta kafa, sakamakon tashe tashen hankula da ake dangantawa da ayyukan kungiyar ta Boko Haram. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China