in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kasaitaccen bikin murnar sabuwar shekarar Sinawa a kwalejin confucius ta jami'ar Lagos a Nijeriya
2014-01-30 16:13:21 cri

A ranar 29 ga wata, aka yi kasaitaccen bikin murnar sabuwar shekara ta Sinawa a kwalejin confucius ta jami'ar Lagos da ke Tarayyar Nijeriya. Mataimakin karamin jakadan Sin da ke jihar Lagos da karamin jakadan Faransa a jihar da wakilin karamin ofishin jakadancin Amurka da kuma wakilan masana'antun kasar Sin da al'ummar Sinawa da shugabannin jami'ar duk sun halarci bikin.

A yayin bikin, malamai Sinawa da dalibai 'yan Nijeriya sun nuna wasannin wake-wake da raye-raye tare da Kongfu, da sauran al'adun Sinawa, abin da yasa bikin ya yi armashi sosai.

Shugaban kwalejin Confucius ta jami'ar Lagos Jiang Lirong tace, kasar Sin na da al'adu sosai, kuma a matsayin wani muhimmin dandali na yada al'adun Sinawa, a cikin shekaru da dama da suka gabata, kwalejin Confucius ya gudanar da ayyuka da dama don sa kaimi ga yin mu'amalar al'adun a tsakanin kasashen Sin da Nijeriya.

A cewarta yanzu haka, a kwalejin Confucius ta jami'ar Lagos, ba ma kawai, a kan koyar da harshen Sinanci ba, har ma ya zama tamkar wata gada ce ta yada al'adun Sinawa.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a ko wane bikin al'adun Sinawa, kwalejin Confucius ta jami'ar Lagos ya kan shirya bukukkuwa, musamman ma a sabuwar shekara ta Sinawa, malamai da dalibai na kwalejin su kan shirya biki, don gayyatar sauran dalibai da malamai na jami'ar da 'yan kasuwa na wurin da Sinawa a Nijeriya domin su halarci bikin, da ake nuna al'adun Sinawa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China