Mukaddashin kakakin MDD Farhan Haq ne, bayyana hakan ga manema labaru a ranar Jumma'a 20 ga watan nan. Faq ya kara da cewa, yayin da ake ci gaba da rabon kayayyakin abinci ga dubban al'ummomin da rikicin kasar Afirka ta Tsakiyan ya ritsa da su a masallatai, da majami'u da asibitoci, a hannu guda wasu mahara da ba a tantance da su ba, na hakon kaiwa asibitoci farmaki.
Cikin watan nan na Disamba kadai, shirin samar da abinci na MDDr ya raba abinci, da yawansa ya doshi tan 506 ga al'ummar kasar sama da 118,000 dake zaune a birnin Bangui.
Rahotannin baya-bayan nan na nuna cewa, tsakanin makwanni Biyu kacal, fadace-fadacen da ke ci gaba da yaduwa a sassan babban birnin kasar Bangui, sun sabbaba tserewar kimanin mutane 210,000, yayin da sama da mutane 710,000 suka rasa matsugunnansu, tun fara rikicin kasar a shekarar da ta gabata har zuwa yanzu, baya kuma ga wasu karin mutane 75,000 da aka ce, sun yi gudun hijira sakamakon halin da kasar ta fada. (Saminu)