Yanzu, bangarorin daban daban ba su fayyace abubuwan da za a tattauna a shawarwarin ba, amma akwai tabbacin cewa, shawarwarin wannan zagaye ya nuna cewa, an shiya shi ne don warware batun nukiliyar kasar cikin dogon lokaci, wato ke nan, an samu ci gaba a yarjejeniyar da aka daddale a shekarar bara. Shawarwari na wannan zagaye wani kwarya-kwaryan taro ne da nufin tuntubawar bangarorin da abin ya shafa, kuma za a tattauna wasu batutuwa a yayin shawarwarin, amma ba a sa ran daddale yarjejeniya a shawarwarin ba.
Tuni, ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa, tawagar kasar Iran za ta yi shawarwari bisa kiyaye hakkin kasar Iran. (Bako)