in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko wace kasa na da ikon zabar dokokin da za su dace da yanayin kasarta, in ji wakilin Sin
2014-02-20 16:27:31 cri
Jiya Laraba 19 ga wata ne, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min ya bayyana a hedkwatar MDD dake birnin New York cewa, ko wace kasa na da ikon zabin tafiyar da harkokinta bisa dokokin da za su dace da yanayin kasar, kuma warware rikici ta hanyar lumana shi ne abin da ya dace bisa doka.

A yayin taron kara wa juna sani da kwamitin sulhu na MDD ya shirya mai taken "inganta da kuma kyautata ayyukan dake shafar gudanar da harkoki bisa dokoki yayin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa ", Wang Min ya bayyana cewa, sabo da bambancin da ke tsakanin kasa da kasa dangane da yanayin bunkasuwar kasa, ba za a iya samun doka daya da za ta dace da dukkanin kasashen duniya ba, ko wace kasa na da ikon zabar gudanar da harkokinta bisa dokokin da za su dace da yanayinta, a sa'i daya kuma, kasashe na iya koyon fasahohin sauran kasashen da abin ya shafa yayin gudanar da harkokinsu na cikin gida, ta yadda za a iya bunkasa tare.

Bugu da kari, Mr. Wang ya jaddada cewa, warware rikici ta hanyar lumana shi ne abin da ya dace bisa doka. Ya ce, idan ana son gudanar da harkoki bisa doka yadda ya kamata kuma cikin dogon lokaci a wasu kasashen dake fama da rikici ko wadanda suka taba fuskantar rikici, ya kamata a inganta ayyukan da abin ya shafa tare da ciyar da ayyukan da ke shafar yunkurin siyasa, bunkasuwar tattalin arziki, zaman lafiyar al'ummomi da dai sauran fannoni gaba tare. Kuma ya kamata a girmama mulkin kan wadannan kasashe da kuma halin da su ke ciki, kana da taimaka musu wajen kara karfinsu na raya kasa da kansu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China