A yayin wannan ziyara, mista Kerry zai gana da firaministan kasar Pakistan Nawaz Sharif da kuma yin shawarwari tare da wasu manyan jami'an kasar dangane da wasu muhimman batutuwan da suka shafi dangantakar kasashen biyu da na shiyyar. Kasashen biyu na fatan farfado da shawarwarin da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare da kuma hadin gwiwarsu a fannin makamashi da sauransu.
Kwanan baya, ma'aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta bayyana cewa, Pakistan za ta dukufa wajen farfado da shawarwarin da ke tsakaninta da kasar Amurka bisa manyan tsare-tsare. Hakazalika, Pakistan zata gabatar da batun farmakin jirgin sama mai sarrafa kansa na kasar Amurka a sararin saman kasar Pakistan a yayin wannan ziyara ta Kerry a kasar. (Maryam)