in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mamnoon Hussain ya cimma nasara a babban zaben shugaban kasar Pakistan
2013-07-31 10:54:34 cri
Ran 30 ga wata da yamma, hukumar zaben kasar Pakistan ta sanar da sakamakon babban zaben shugaban kasar, inda ta nuna cewa, dan takarar jam'iyyar dake mulki a kasar, Muslim League - Nawaz, Manmoon Hussain shi ne yaci nasarar lashe babban zaben, inda hakan ke nuna cewar shine zai zama shugaban kasar, na goma sha biyu.

Mr. Mamnoon Hussain ya cimma nasara ne a zaben da kuri'u 432, yayin da abokin hamayyarsa Wajihuddin Ahmed na jam'iyyar Tehreek-e-Insaf ya samu kuri'u guda 77.

Shugaban kasar na yanzu Asif Ali Zardari zai kammala wa'adin aikinsa ran 8 ga watan Satumba shekarar bana, don haka nan da wata daya za a rantsar da Mr. Mamnoon Hussain a matsayin shugaban kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China