A yayin ganawarsu, Mista Wang ya bayyana cewa, a bana aka cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Angola. Don haka gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da fatan za su kara amincewa da juna a fannin siyasa, da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a kan harkokin duniya da na shiyya shiyya, a kokarin kara kyautata dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, ta yadda za a kara kawo alheri ga jama'arsu a nan gaba.
A nasa bangare, Mr Georges Chikoti ya ce, a cikin wadannan shekaru 30, dangantaka tsakanin Angola da Sin na bunkasa lami lafiya, tare da samun ci gaba sosai. Ya ce Sin ta yi kokarin shiga yunkurin farfado da Angola bayan yaki, inda kamfanonin Sin suka ba da babbar gudummawa a fannoni daban daban wajen raya tattalin arziki da kyautata rayuwar jama'ar Angola. A sabili da haka, kasar Angola na fatan cewa, dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu za ta kara bunkasa yadda ya kamata.(Fatima)