Idan aka kwatanta hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen EU da Rasha a fannin sararin samaniya, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka a bangaren nazarin sararin samaniya yana baya-baya. Yarjejeniyar Wolfe ta kawo cikas game da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a wannan fanni, domin wannan yarjejeniya ta hana hadin gwiwar dake tsakanin hukumar sararin samaniya ta Amurka da ta Sin, kuma ta hana hukumar ta gayyaci jami'an gwamnatin Sin domin su ziyarci hukumar.
A wannan rana, yayin da Xu Dazhe ya ambaci cikas din da Amurka ta kawo game da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, ya ce, manufar da kasar Sin take bi a fannin nazarin sararin samaniya tana da kyau, sabo da fasahar sararin samaniya ta Amurka tana sahon gaba a duniya, kasar Sin tana fatan inganta hadin gwiwa da kasashen duniya, ciki har da Amurka. Yu Dazhe ya ci gaba da bayyana cewa, kasar Sin ta nace kan manufar raya nazarin sararin samaniya cikin lumana, kuma tana adawa da yin hamayya wajen binciken sararin samaniya, kuma za ta dauki hakikanin mataki wajen kiyaye muhalli a sararin samaniya, kana za ta ci gaba da inganta mu'amala da hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasashen duniya. (Bako)