in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Amurka za ta kai kara ga mutumin da ya sanya wuta ga karamin ofishin jakadancin Sin a San Francisco
2014-01-07 15:38:12 cri
Gwamnatin Amurka ta fara kai kara ga dan asalin kasar Sin mai suna Feng Yanfeng da ya sanya wuta a babbar kotun tarayya da ke yankin arewacin Californiya, bayan ya kai kansa ga hukumar 'yan sanda tare amsa da laifin sanya wuta ga babbar kofar karamin ofishin jakadancin Sin a San Francisco a ranar 1 ga wata da dare.

A ranar 4 ga wata, bisa takardar karar da ofishin bincike na tarayyar Amurka a yankin San Francisco ya bayar, an ce, an zargi Feng Yanfeng da ya aikata laifuffuka guda 2 da suka hada da sanya wuta da ganga da kuma laifin lalata kadarorin gwamnatocin kasashen waje da kungiyoyin kasa da kasa da jami'an kasashen waje dake Amurka.

A ranar 1 ga wata da dare, mista Feng Yanfeng ya zubar man gangunan fetur 2 a kofar shiga ta karamin ofishin jakadancin Sin a San Francisco, tare da sanya wuta, lamarin da ya haddasa lalata babbar kofar karamin ofishin jakadancin Sin a San Francisco. Feng Yanfeng, dan asilin kasar Sin ya samu takardar zama a Amurka a shekarar 2004. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China