in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dankon zumunta da ke tsakanin shugabannin Sin da Rasha ya yi matukar jawo hankalin duniya
2014-02-07 16:34:16 cri

A ranar 6 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, kuma wannan shi ne aiki na farko da shugaba Xi ya yi cikin ziyararsa a birnin Sochi.

Shugabannin kasashen biyu sun nuna cewa, a cikin sabuwar shekara, za a kara ingiza dangantakar kasashen biyu, inda suka cimma daidaito game da hadin gwiwa dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, a kan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya.

Bayan taron, shugabannin kasashen biyu sun yi magana ta hoton bidiyo tare da shugabannin jirgin ruwan yaki na kasashensu, da ke aikin rakiya da ba da kariya ga makaman kasar Syria da ake shirin lalatawa.

"Shugabannin Xi Jinping da Vladimir Putin, jirgin ruwan yaki na Yancheng ya dauki nauyin rakiyar makaman kasar Siriya. Ya zuwa yanzu, an gudanar da wannan aiki yadda ya kamata, muna yin mu'amala da hadin gwiwa da kasar Rasha cikin aminci."

A ranar 6 ga wata da yamma, shugaban jirgin ruwan yaki na Yancheng mallakar kasar Sin, da ke ba da kariya a tekun Mediterranean Li Pengcheng, da shugaban jirgin ruwan yakin "Peter the great" na kasar Rasha Peshkulov, sun bayyanawa shugabannin Sin da Rasha halin da ake ciki game da aikin da suke gudanarwa.

A watan Satumba na shekarar 2013, kungiyar hana yaduwar makamai masu guba ta duniya, da kwamitin sulhu na M.D.D. suka zartas da kuduri, wanda ke kunshe da aniyar sufurin makamai masu guba mallakar Siriya zuwa jirgin ruwa na kasar Amurka, don lalata su. Inda aka amince kasashen Sin da Rasha su tura jiragen ruwan yaki, don ba da kariya ga wannan aiki.

Daga watan Janairun bana kawo wannan lokaci, jirgin ruwan yaki mai suna Yancheng mallakar kasar Sin, ya kammala aikin ba da kariya har sau biyu.

Game da hadin gwiwa tsakanin sojojin ruwa na kasashen Sin da Rasha, a wannan rana, yayin da shugabannin Xi da Putin ke zantawa da shugabannin jiragen ruwan yaki na kasashen biyu, sun jaddada cewa, aikin ba da kariya da kasashen biyu suke yi, ya ba da babbar gudummawa game da warware batun Siriya ta hanyar siyasa, kuma kasashen biyu za su ci gaba da dukufa ka'in da na'in, wajen tabbatar da zaman lafiya da karko a shiyya-shiyya, da ma dukkanin duniya baki daya.

"Kasashen Sin da Rasha sun yi kokari sosai domin warware batun Siriya cikin lumana, da lalata makamai masu guba mallakar kasar, kuma sojojin ruwan kasashen biyu sun dauki babban nauyi, don tabbatar da tsaron wannan aiki, nan gaba za su ci gaba da kokari, muna fatan sojojin ruwa za su kammala ayyukan na su cikin nasara."

"Tun daga karshen shekarar bara, kun dauki nauyin ba da kariya ga lalata makamai masu guba na Siriya bisa kundin tsarin mulkin M.D.D. da kuduran da suka shafi hakan na kwamitin sulhun majalissar. Muna fata za ku kammala ayyukanku cikin nasara, da kara ba da gudummawa game da lalata makamai masu guba na Siriya lami lafiya, da warware batun Siriya ta hanyar siyasa."

Idan aka waiwayi shekarar da ta gabata, kasashen Sin da Rasha sun cimma nasara hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki, aikin soji da batun kasa da kasa, kuma dankon zumunci da ke tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ya jawo hankalin jama'a sosai. Tun daga farkon shekarar 2014, Rasha ta zamanto zango na farko da shugaba Xi ya sauka, a ziyarar da ya gudanar a ketare.

A ranar 6 ga wata da yamma, yayin da shugaba Xi ke ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, ya yi murmushi yayin da yake cewa, ya zo Rasha musamman don taya mata murna, "A yayin bikin gargajiya na Sinawa, mun zo halartar bikin bude gasar wasannin Olympic na lokacin sanyi da za a fara a Sochi, wannan ya zama bukukuwan murna guda 2 gare mu. Bisa al'adun Sinawa, idan makwabta ko abokanka suka shirya biki, dole ne a je taya musu murna, sabo da an ce, "Zuwa da kai, ya fi sako", shi ya sa, na zo don taya Rasha murna."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China