in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya tashi daga Beijing zuwa Sochi na Rasha
2014-02-06 16:59:31 cri
Bisa gayyatar da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing yau 6 ga wata zuwa birnin Sochi na Rasha, inda zai halarci bikin bude gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi karo na 22.

Wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya halarci manyan gasannin motsa jiki da aka gudanar da su a kasashen ketare. A lokacin da yake birnin Sochi, shugaba Xi zai halarci bikin bude gasar da liyafar maraba da dai sauransu, tare da ganawa da 'yan wasan kasar Sin 139 da za su shiga gasar.

Za a gudanar da gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi karo na 22 daga ranar 7 zuwa 23 ga wata a birnin Sochi da ke gabar tekun Black Sea.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China