in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da shirye shiryen bude wasannin Olympic a birnin Sochi
2014-02-05 16:19:53 cri
A ci gaba da shirye shiryen bude gasar Olympic na lokacin sanyi karo na 22 dake tafe a kasar Rasha, an yaye kallen wani gini dake alamta alkawarin tsagaita husuma, a ranar Talata 4 ga watan nan, a wani wajen shakatawa dake birnin Sochin kasar ta Rasha.

Bikin wanda ya samu halartar shugaban hukumar gudanar da wasannin na Olympic Thomas Bach, da mataimakin Firaministan kasar Rasha Dmitry Kozak, da ragowar masu ruwa da tsaki, a cewar Mr. Bach na da nufin tabbatar da wannan gasa, a matsayin wata hanyar bunkasa zaman lafiya da lumana tsakankanin al'ummar duniya.

Shi ma a nasa jawabi yayin wannan biki mataimakin Firaministan kasar Rasha Dmitry Kozak, cewa ya yi gasar Olympic sahihiyar hanya ce da ke baiwa 'yan siyasa, da sassan da ba sa ga maciji da juna damar sulhuntawa, don haka akwai bukatar ci gaban wanzuwarsa a wannan lokaci. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China