Mataimakin tawagar wakilan kasar Xiao Tian da yanzu haka suka bar nan Beijing zuwa Sochi ya bayyana cewa yanayin wajen ba ya da banbanci da gida.
Yana mai bayanin jim kadan bayan kaddamar da tutar kasar a sansanin wasannin cewa dakin cin abinci ya yi matukar burge su saboda akwai sashin abinci har da nahiyar Asiya kuma wuraren kwana ma an kawata su da abin da ya kamata.
Mr. Xiao musamman ya nuna yabo game da tazaran filin wasan da kuma masaukin 'yan wasan wanda a cewarsa suka yi kusa da juna, abin da zai taimaka ma 'yan wasan samar da sakamako mai kyau.
Har ilar yau Jami'in ya yi nuni da cewa sansanin wasannin na Sochi ya kai matsayin da ake bukata. (Fatimah Jibril)