Wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin zai halarci manyan gasannin motsa jiki da ake gudanar da su a kasashen ketare. A lokacin da yake birnin Sochi, shugaba Xi zai halarci bikin bude gasar da liyafar maraba da dai sauransu, tare da ganawa da 'yan wasan kasar Sin 139 da za su shiga gasar da kuma shugabannin kasa da kasa da na kungiyoyin kasa da kasa.
Za a gudanar da gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi karo na 22 daga ranar 7 zuwa 23 ga wata a birnin Sochi da ke gabar tekun Black Sea.(Tasallah)