A cewar kakakin majalissar Mertin Nesirky, Mr. Ban zai yi amfani da wannan dama wajen ganawa da sauran shugabanni da za su halarci bikin wanda za a gudanar a ranar Juma'a 7 ga watan nan na Fabarairu a birnin Sochin kasar ta Rasha.
Haka zalika bikin na bana zai baiwa Mr. Ban damar gabatar da jawabi ga mambobin babban kwamitin shirya wasannin Olympic na kasa da kasa wato IOC.
Nesirky ya kara da cewa alakar dake tsakanin MDD da kwamitin IOC na samun tagomashi, wanda hakan na daya daga manyan dalilan da suka sanya babban magatakardan majalissar bayyana aniyyarsa ta halartar wannan biki.
Ana dai sa ran gudanar da gasannin Olympic din na bana ne tsakanin 7 zuwa 23 ga watan nan da muke ciki. Sa'an nan wasannin Olympic na ajin nakasassu karo na 11 ya biyo baya, daga 7 zuwa 16 ga watan Maris dake tafe, duka dai a birnin na Sochi. (Saminu Alhassan)