Wakilan kasashe mambobin kwamitin tsaro na MDD da suka hada da kasashen Sin, Rasha, Amurka, Faransa, Burtaniya tare kuma da kasar Jamus sun sake komawa kan tebur a ranar Laraba a Geneva a wani sabon zagayen shawarwari tare da kasar Iran kan shirinta na nukiliya da ya kamata a kammala a ranar Jumm'a.
Gungun P5+1 na karkashin wakilcin madam Catherine Asthon.
Wannan tattaunawa ta zo kwanaki goma bayan zagayen tattaunawar da ta gabata tsakanin wakalan P5+1 da kasar Iran. Daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Nuwamba, gungun kasashe biyar tare da Jamus da ita kasar Iran sun yi kokari a lokacin da ba'a zata domin cimma wata mafita kan batun nukiliya na kasar Iran, kokarin da ya kare kan tashe baran baran, duk karin rana guda da aka yi domin tsawaita shawarwarin.
Shawarwarin kan batun nukiliyan Iran sun tsaya wuri guda a tsawon lokaci ba tare da cimma wata mafita ba, duk da yawan shawarwarin da aka yi ta gudanarwa, dalilin rashin yarda tsakanin Iran da kasashen Yammacin duniya.
Kasashen dai na zargin Teheran da yin amfani da shirinta na nukiliya domin karfafa karfin makamanta, zargin da gwamnatin Iran ta yi watsi da shi dake bayyana 'yancin Iran na sarrafa makamashin nukiliya domin amfanin jama'a. (Maman Ada)