in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatan Sin 2 da ke Kadunar Nijeriya sun ji rauni sakamakon farmakin da aka kai musu
2014-01-26 15:48:06 cri

A ran 24 ga wata, wasu mutane da ba a san asalinsu ba sun kai farmaki a jihar Kaduna da ke arewacin kasar Nijeriya, wanda ya sanya ma'aikata biyu na kamfanin kasar Sin suka ji rauni.

A ran nan da safe, a kan hanyarsu zuwa wurin aiki, ma'aikatan wani kamfanin kasar Sin sun gamu da farmakin da aka kai musu da bindigogi, amma ba a san asalinsu ba, wannan dai ya sanya ma'aikata biyu Sinawa suka ji rauni tare da jikkata sauran ma'aikata 'yan Nijeriya guda 3. Bayan farmakin, 'yan fashi sun gudu da sauri, amma ba su kwace dukiyoyi ko kayayyaki ba. A halin yanzu dai, wannan kamfanin Sin ya riga ya dakatar da aiki a wurin, dukkan ma'aikatansu sun riga sun koma sansaninsu, kuma sun kara tura 'yan sanda don inganta aikin tsaro a sansanin.

Daga ya samu labarin, ofishin jakadancin Sin da ke Nijeriya ya kadammar da tsarin daidaita matsala cikin gaggawa nan take, ya taimakawa kamfanin Sin wajen kai da mutanen da suka ji rauni zuwa asibiti, kuma ya tumtubi karamar gwamnatin Kaduna, da hukumar 'yan sandan jihar, don bukace su da su tabbatar da tsaron kamfanonin Sin da ma'aikatan Sin a wurin. A halin yanzu dai, wadannan ma'aikata biyu da suka ji rauni suna samun jinya a asibitin da ke birnin Abuja, babban birnin kasar Nijeriya, yanzu sun sami sauki a hankali, ofishin jakadancin Sin da ke Nijeriya ya riga ya tura jami'ai zuwa asibitin domin nuna jejeto. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China